• Home  
  • Najeriya Ta Buƙaci MDD Ta Kawo Ƙarshen Yaƙi Tsakanin Iran Da Isra’ila 
- Babban Labari - Kasashen Ketare - Labarai

Najeriya Ta Buƙaci MDD Ta Kawo Ƙarshen Yaƙi Tsakanin Iran Da Isra’ila 

Ma’aikatar harokokin wajen Najeriya ta ce bata ji daɗin abin da Isra’ila ta yi na kai wa maadanar makaman Iran Hari ba. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Ma’aikatar harokokin wajen Najeriya ta ce bata ji daɗin abin da Isra’ila ta yi na kai wa maadanar makaman Iran Hari ba. 

Gwamnatin Najeriyar ta yi kira ga ƙasar Isra’ila da Iran da su kai “zuciya nesa” don dawo da zaman lafiya.

Gwamnatin Najeriya ta yi Alla-wadai da harin da Isra’ila ta kai wa Iran, abin da ya janyo ƙazantar rikici tsakanin ƙasashen biyu.

Najeriya ta ce, ci gaba da kai hari da kuma ramuwa tsakanin ƙasashen biyu, yana ƙara saka rayukan fararen hula cikin barazana.

Haka zalika rikicin na ƙasashen biyu 2 a cewar gwamnatin Najeriya zai ƙara jefa Gabas Ta Tsakiya cikin bala’i.

“A matsayin mu na ƙasar da ke son zaman lafiya, da ganin kyautatuwar hulɗar diflomasiyya, muna kira ga dukkan ɓangarori da ke rikici da su fifita tattaunawa maimakon faɗa da juna,” in ji sanarwar.

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ɗauki matakan laluɓo hanyar warware rikicin.

“Ɗaukar matakin soji ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai