NLC Za Ta Fara Zanga-zanga Ranar 4 Ga Fabarairun 2025

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta sanar da 4 ga Fabarairun 2025, a matsayin ranar da zata fara zanga zangar gama gari a Najeriya domin nuna fushinta akan karin kuɗin kiran waya da na Data da kaso 50 cikin 100.

NLC ta sanar da matsayar ne a wata sanarwa data fitar a Abuja yammacin ranar Laraba bayan kammala taronta na majalisar zartaswa.

A ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2025 NLC tayi watsi da karin kuɗin kiran waya da Data da Kamfanonin sadarwa suka yi a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC a ranar 20 ga watan Janairu, 2025, ta sanar da amincewarta ga kamfanonin sadarwa su ƙara kuɗin kiran waya da na Data da kashi 50 cikin dari.

Amincewar NCC ta janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasa da ita kanta Ƙungiyar ta Kwadago Inda ta yi watsi da karin kuma tayi barazanar shiga zanga-zanga da ƙauracewa amfani da hanyoyin sadarwa na Kamfanoni muddin ba’a koma yadda ake a baya ba.

NLC tace za a yi zanga-zangar ne a matsayin gargaɗi ga gwamnati da bayyana mata cewa ma’aikata sun bijirewa karin

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda