NNPCL ya ƙulla yarjejeniyar gyara matatun man fetur na Warri da Fatakwal

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPCL ya rattaba hannu kan yarjejeniyar kammala aikin gyara matatun mai na Fatakwal da ke Jihar Ribas da kuma ta Warri da ke Jihar Delta.

Yarjejeniyar da NNPCL ɗin ya ƙulla da wasu kamfanonin China biyu domin kammala matatun na zuwa ne bayan gaza ƙarasa aikin da ya laƙume dala biliyan 2.39 a baya.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce yarjejeniyar za ta samar da abokan hulɗa da za su taimaka wajen farfaɗo da matatun da kuma bunƙasa harkokin sarrafa mai da masana’antun sinadarai.

Ko da yake gwamnati ta kashe biliyoyin daloli wajen gyaran matatun a baya, ciki har da wanda aka ce ya fara aiki a Fatakwal kafin ya sake tsayawa, har yanzu ba a bayyana adadin kuɗin da za a kashe a sabon shirin ba.

NNPCL ta bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba na neman ɗorewar aiki da riba a matatun mai na ƙasar, tare da jaddada cewa ana ci gaba da tattaunawa kafin cimma cikakkiyar yarjejeniya.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Oyo ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 10

Majalisar Dattawan Amurka ta kaɗa ƙuri’ar haramta wa Trump yaƙi da Iran

CP Bakori ya umarci dakarun rundunar su ƙara faɗaɗa sintiri da dogaro da bayanan sirri.