NOA da JCI Abuja Unity sun ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a kan tsaron hanya

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, tare da hadin gwiwar ƙungiyar Junior Chamber International, JCI, reshen Abuja Unity, sun shirya wayar da kan ’yan Najeriya kan muhimmancin kiyaye dokokin hanya da kuma zama ’yan ƙasa nagari.

Daraktan yaɗa labarai da Sadarwa na hukumar NOA, Bala Musa, ya ce an gudanar da shirin ne ƙarƙashinshirin “Road Safety and You”, wato “Tsaron Hanya da Kai”, a zauren taro na hukumar da ke Abuja.

Shirin ya samu halartar wakilan hukumomin gwamnati, hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, jami’an tsaro, masu harkar inshora, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Daraktar sadar da jama’a kan tsaron al’umma da bin doka ta NOA, Barrista Tessy Nnalue, ta jaddada muhimmancin ci gaba da wayar da kan jama’a game da haɗurran ababen hawa.

Ta ce ɗaukar matakan kariya da bin dokokin hanya na iya taimakawa wajen rage haɗurran da ake iya kauce musu da rasa rayuka.

A yayin taron, wakilan Nigerian Council of Registered Insurance Brokers, NCRIB, da Vehicle Inspection Office, VIO, da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, sun yi bayani kan inshorar motoci, lafiyar ababen hawa, tuƙi cikin aminci da kuma hanyoyin hana haɗari.

Mahalarta sun kuma samu shawarwari kan muhimmancin kula da motoci akai-akai, musamman tabbatar da birki, fitilu da tayoyi suna cikin yanayi mai kyau, da kuma samun ingantattun takardun mota.

An kuma ja hankalinsu kan guje wa gudun wuce gona da iri, amfani da waya yayin tuƙi, da kuma tuƙi yayin maye.

Shirin ya ƙunshi wasan kwaikwayo, tattaunawa tsakanin ƙwararru da kuma zaman tambayoyi da amsoshi, inda mahalarta suka samu damar neman ƙarin bayani kan dokokin hanya, inshora da matakan da ya kamata a ɗauka bayan aukuwar haɗari.

Masu shirya taron sun buƙaci mahalarta su zama jakadun tsaron hanya, tare da yaɗa saƙonnin wayar da kai a cikin al’ummominsu, domin ƙarfafa haƙuri, taka-tsantsan da mutunta rayuwar masu amfani da hanya.

Post masu alaƙa

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci