Ƴan majalisar wakilai 8 na Kano sun fice daga NNPP zuwa APC

Ƴan Majalisar Wakilai takwas daga Jihar Kano sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar NPP zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar jihar.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya sheƙar a hukumance yayin zaman majalisar a yau Talata, bayan karanta wasiƙun da ‘yan majalisar suka aike wa zauren.

A cikin wasiƙun nasu daban-daban, ‘yan majalisar sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar NNPP ne ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki.

Wannan sauyin ya samu halartar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau Jibrin, da tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan ‘yan siyasa.

‘Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Tijjani Abdulkadir Jobe (Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa), Garba Ibrahim Diso (Gwale), Hassan Shehu Hussain (Nassarawa), Idris Dankawu (Kumbotso), Muhamamad Chiroma Nalaraba (Gezawa/Gabasawa), Barr. Rabiu Yusuf (Takai/Sumaila), Dr. Ghali Mustapha Tijjani (Albasu/Gaya/Ajingi) da Barr. Muhammad Bello Shehu (Fagge).

Post masu alaƙa

DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa

An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma