NOA ta buƙaci ICAN ta sanya gaskiya da kyawawan ɗabi’u a aikita na akanta

Shugaban hukumar wayar da kai ta ƙasa NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya buƙaci  ICAN da su mayar hankali wajen ɗabbaƙa kyawawan ɗabi’un kishin ƙasa a matsayin muhimmin ɓangare na aikinsu a faɗin Najeriya.

Ya bayyana sana’ar akanta a matsayin ginshiƙi wajen inganta gaskiya, riƙon amana da kuma bayyana gaskiya a tsarin tattalin arziki.

Sanarwar ta fito ne ta bakin Mallam Bala Musa, Daraktan Sadarwa da Yaɗa Labarai na NOA.

An bayyana hakan ne a taron Makon Lissafi na Abuja 2026 mai taken jaddada dabi’u da ƙwarewa a matsayin tubalin ci gaban al’umma da tattalin arziki.

A nasa jawabin maraba, shugaban ICAN, Dakta Michael Nnachi Okpara, ya jaddada buƙatar samun ƙwararru a matsayin wata hanya ta inganta ɗabi’u

Post masu alaƙa

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC