Ƴan sanda sun tsaurara tsaro a cibiyoyin JAMB jihar a Jigawa

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Haruna A. Yahaya, ya kai ziyara cibiyoyin rubuta jarrabawar JAMB, don duba  yanayin tsaron wuraren da ake gudanar jarrabawar.

Ziyarar tasa na da nufin tabbatar da cewa an gudanar da jarrabawar cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma bin tsari, ba tare da an samu wata matsala ba.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar asabar.

Sanarwar ta ce kwamishinan  ƴan sandan ya yaba da yadda jami’an tsaron  ke gudanar da aikin bayar da tsaro, ya tabbatar da cewa duk wanda yayi yunkurin tayar da hankalin al’umma ba za a saurara masa ba.

A ƙarshe rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa a shirye wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.