Darakta Janar na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya tabbatar wa ma’aikatan hukumar cewa inganta walwalarsu da haɓaka ƙwarewarsu na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, domin gina ma’aikata masu ƙwazo da nagarta da za su ci gaba da ciyar da manufofin hukumar gaba.
Issa-Onilu ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar a hedikwatar NOA da ke Abuja.
Ya yaba wa shugabanni da ma’aikatan hukumar bisa irin goyon baya da haɗin kan da suka ba shi tun bayan da ya karɓi ragamar jagoranci shekaru biyu da rabi da suka gabata.
A cewarsa, wannan haɗin kai ya taimaka matuƙa wajen sake farfaɗo da hukumar tare da ƙarfafa rawar da take takawa wajen wayar da kan ‘yan Najeriya.
Ya ce yanzu NOA ta zama hukuma mai tasiri wajen inganta ɗabi’u nagari, ƙarfafa kishin ƙasa da kuma wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
A matsayin misali, ya ambaci shirin National Values Charter, wanda ya ce tallan sa ya samu damar isa ga miliyoyin masu kallo bayan an riƙa haska shi a lokacin wasannin Gasar Firimiya ta Ingila da kuma Gasar Zakarun Turai ta UEFA.
Ya ce hakan ya taimaka wajen yaɗa saƙon kishin ƙasa, ɗa’a da alhakin zama nagartaccen ɗan ƙasa ga dimbin jama’a a Najeriya da ma ƙasashen waje.
Darakta Janar ɗin ya kuma ce daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar akwai fara amfani da jarabawar kwamfuta (CBT) wajen tantance ma’aikatan da ke neman karin girma. Ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bai wa ƙwarewa muhimmancin da ta dace.
Issa-Onilu ya kuma bayyana cewa kudirin sabuwar dokar NOA ya tsallake karatu na farko a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai. Ya ƙara da cewa hukumar na ci gaba da ƙulla haɗin gwiwa da manyan kamfanoni da ƙungiyoyi domin tallafa wa shirye-shiryenta na wayar da kan jama’a, inganta ɗabi’u da ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da saka hannun jari wajen horas da ma’aikata, haɓaka ƙwarewarsu da kuma inganta walwalarsu, domin su kasance cikin shirin fuskantar sauye-sauyen da ke tattare da aikin hukumar.
Tun da farko, Daraktar Sashen Albarkatun Jama’a da Gudanarwa, Ayisola Olowoyo, ta yaba wa Darakta Janar bisa ci gaba da shirya tarurrukan tattaunawa da ma’aikata, tana mai cewa hakan ya samar da damar musayar ra’ayi, karɓar shawarwari da kuma inganta ayyukan hukumar.
Haka kuma, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na hukumar sun yaba da salon jagorancin Issa-Onilu da kulawar da yake bai wa walwalar ma’aikata. Sai dai sun buƙaci a ƙara tallafa wa ma’aikatan da suka yi rashin ‘yan uwa, iyalan ma’aikatan da suka rasu da kuma waɗanda suka yi ritaya.
Taron ya samu halartar daraktoci daga sassa daban-daban na hukumar da ma’aikatan hedikwata, lamarin da ya nuna ƙudirin shugabancin NOA na ci gaba da bunƙasa tattaunawa da haɗin kai a tsakanin ma’aikata domin ƙara inganta ayyukan hukumar.