Home » Rahoto: Illar Tsuga Gishiri a Cikin Abinci

Rahoto: Illar Tsuga Gishiri a Cikin Abinci

LAFIYA/GAME DA AMFANI DA GISHIRI

by Anas Dansalma
0 comment Minti 1 read

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi wani jan kunne game da yawan tsuga gishiri a cikin abinci

Saboda a cewarta rashin cin abinci mai gina jiki na haifar da mutuwar mutane kamar yadda tsuga gishiri ke yin irin wancan makamanciyar illa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoto kan amfani da sinadarin da a Turance ake kira da Sodium, wato gishiri a wani shiri na rage amfani da gishirin da kaso talatin cikin ɗari daga nan zuwa shekarar 2025.

Hukumar ta kuma ba da shawara kan gaggauta rage amfani da gishirin domin kuwa yin hakan zai taimaka wajen ceton rayuka ku san miliyan bakwai a faɗin duniya a tsakankanin shekarar da muke ciki zuwa 2030.

Tare da jan hankalin hukumomi a duniya kan yin dokoki da za su tilasta rage amfani da gishirin domin hana al’ummarsu kamuwa da cututtuka da ke shafar zuciya da haifar da matsalar katsewar bugun jini da ma wasu ƙarin matsaloli da kan shafi lafiya.

Hukumar ta kuma ƙara da cewa adadin gishirin da ake amfani da shi a kowacce rana a duniya ya kai gram 10 da ɗigo 8 sama da yadda hukumar ta shawarta na amfani da gram biyar koma cokalin zuba shuga na

Haka kuma ƙasashe tara ne a kaf faɗin duniya a yanzu da ke da wasu dokoki da ke lura da yadda ake amfani da gishiri da duniya.

Waɗannan ƙasashe sun haɗa Brazil, Chile, Czech Republic, Lithuania, Malaysia, Mexico, Saudi Arabia, Spain da kuma Uruguay

A ƙarshe hukumar ta yi jan hankali kan a yakamata masu samar da kayan abinci ko na sarrafa abinci da su riƙa ayyana adadin gishirin da ke cikin abincin nasu

Wannan zai taimaka wa al’umma fahimtar adadin gishirin da suke amfani da shi a kowanne nau’in abinci da za su saya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?