A yayin da ake kai azumi na shida a yau, al’umma na cigaba da nuna damuwa game da farashin ƙanƙara wanda sukan yi amfani da ita domin sanyaya abin sha a lokacin buɗa baki.
Su ma masu sana’ar sun bayyana wa abokiyar aikinmu irin ƙalubalen da suke fuskanta, musamman a lokacin da ake fama da ƙarancin wutar lantarki da tsadar kayan alkinta ƙanƙara da makamantansu.
Har’ila yau wani masanin lafiya yi mana ƙarin haske kan matsayin amfani da ƙanƙara a lokacin buɗa baki a wannan watan na ramadana.
Ga abokiyar aiki Zubaida Abubakar Ahmad da rahoton da ta haɗa mana.