Ribar da muke ci ta ragu da Naira biliyan 720 a watan Yuli – NNPCL

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ce ya tafka babbar asara inda ribar da ya ci ta Naira biliyan 905 a watan Yuni ta ragu zuwa Naira biliyan 185 a watan Yulin da ya gabata.

Hakan dai na. nufin ribar kamfanin ta fadi da kimanin kaso 79.6 cikin 100.

Kamfanin, a cikin rahotonsa na wata-wata da ya fitar ranar Alhamis, ya ce ya yi jimillar cinikin Naira tiriliyan 4.41 a watan Yuli, sabanin na Naira tiriliyan 4.57 da ya yi a watan da ya gabace shi.

NNPCL ya kuma ce ribar da ya samu a watan Yuni ita ce biliyan 905, ta watan Mayu kuma tiriliyan 1.05, yayin da a watan Afrilu kuma ya ci ribar biliyan 962.

Alkaluman dai sun nuna ainihin faduwa a kudaden shigar kamfanin, duk kuwa da cewa adadin danyen man da kasar ke haka ya karu daga ganga miliyan 1.68 a kullum zuwa ganga miliyan 1.7.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya