Nijeriya Ta Kori Yan Kasashen Waje 102 Bisa Laifin Damfara Ta Intanet

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta mayar da ’yan ƙasashen waje 102 gida, waɗanda suka haɗa da ’yan China 60 da ’yan Philippines 39, bayan kama su da laifin damfara ta intanet.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, EFCC, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis.

A cewar mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, tun da farko an kori ’yan China 50, daga bisani kuma aka samu ƙarin wasu ’yan China 10 da kuma mutum biyu daga ƙasar Kazakhstan tun bayan ƙaddamar da wannan aiki a ranar 15 ga watan Agusta.

Yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, Oyewale ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da mayar da baƙin gida wadanda aka kama da irin waɗannan laifuka a nan gaba.

Bayanai sun ce waɗanda aka korar na cikin mutum 792 da aka kama a Legas bisa zargin damfara ta intanet a watan Disamban da ya gabata.

Aƙalla mutum 192 daga cikin waɗanda aka kama asalinsu ’yan asalin ƙasashen ƙetare ne, kuma daga ciki akwai mutum 148 ’yan ƙasar China ne.

Nijeriya ta yi ƙaurin suna kan damfara ta intanet, wanda ake wa laƙabi da Yahoo-Yahoo, inda hukumar EFCC ke ƙoƙarin daƙile matsalar wadda har yanzu ke ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.

A kwanakin baya, hukumar ta sanar da bankaɗo cibiyoyin koyar da matasa irin wannan damfara ta intanet.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda