Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama motoci marasa lamba 81 a Operation Clean Plates

Rundunar yan sandan jihar Kano ta fara wani aiki na musamman mai suna “Operation Clean Plates”, domin dakile zirga-zirgar motocin da ba su da lambar ko kuma waɗanda aka rufe lambobinsu.

Da yake yi wa manema labarai karin haske, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta lura cewa wasu masu aikata laifuka na amfani da irin waɗannan motoci wajen aikata miyagun laifuka, saboda ba a iya tantance motocin.

Ya ce kafin fara wannan aiki, sai da rundunar ta wayar da kan jama’a ta gidajen rediyo da talabijin, da kuma kafafen sada zumunta, inda ta yi kira ga masu motoci su yi sanyawa motocinsu lamba yadda ya kamata.

Kwamishinan ya ce ya zuwa yanzu, an kama motoci guda 81 da aka samu sun saɓa wa dokar amfani da lambobin rajista, kuma za a gurfanar da direbobinsu a gaban kotu.

Sannan ya ce an kuma tsare wasu motoci uku, bayan masu su sun kasa gabatar da gamsassun bayanai kan mallakarsu da kuma yadda suke amfani da su ya ce bincike na ci gaba a kansu.

CP Ibrahim Adamu Bakori ya jaddada cewa wannan aiki ba don takurawa jama’a aka ƙaddamar da shi ba, sai dai domin ƙara tabbatar da tsaro da kuma hana masu aikata laifuka samun damar ɓuya a cikin al’umma.

Ya kuma yi kira ga masu motoci su tabbatar da cewa motocinsu suna da ingantattun lambobin rajista da aka sanya a fili, tare da cire duk wani abu da ke rufe lambar mota.

Haka kuma, ya buƙaci al’umma su ci gaba da ba rundunar ‘yan sanda haɗin kai, tare da kai rahoton duk wani jami’in da ya yi amfani da wannan aiki wajen muzgunawa jama’a.

A ƙarshe, Kwamishinan ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da Operation Clean Plates a faɗin Jihar Kano.

Post masu alaƙa

Najeriya za ta binciki kamfanonin sada zumunta na Meta, X da AI

Za a kwaso ’yan Najeriya kusan 300 daga Afirka ta Kudu ranar Laraba

Akwai haɗa bakin ƴan cikin gida a harƙallar hukumar bogi