Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake Kano, ta buƙaci jama’a su kasance masu kaucewa dukkan wani abu da zai tayar da tarzoma lokacin gudanar da zaɓe.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan shiyar, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Wannan na zuwa ne a ci gaba da bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026, inda ake ci gaba da wayar da kan al’umma a kasuwanni da kuma tashoshin mota.
Haka zalika, an wayar da kan direbobi kan muhimmancin yin tuƙi cikin nutsuwa, da bin dokokin hanya da kuma guje wa gudun wuce ƙima ko tuƙin ganganci, da duba lafiyar ababen hawansu kafin tafiya.
Gangamin wayar da kan ya samu halartar shugabannin tashar motar Kofar Ruwa da direbobi da sauran al’umma,wanda hakan yake nuna kyakkyawar alaƙar dake tsakanin al’umma da kuma ƴan sanda.
Rundunar ƴan sandan ta jaddada kudurinta na ci gaba da wayar da kai da ƙara inganta hanyoyin hulɗa da jama’a domin inganta tsaro da zaman lafiyar al’umma.