Lauyoyin gwamnatin Kano za su fara gabatar da shaidu kan zargin kisan gillar matar aure da ƴayan ta 6

Gwamnatin jihar Kano, ta bayyana cewa ta kammala shirin fara gabatar da shaidun ta, kan mutanen da ake zargi da kisan kan matar aure Fatima Abubakar da yayanta shida, a unguwar Chiranci Darayi.

Lauyan gwamnatin jihar Kano, barista S.M.Tahir, ne ya bayyana hakan bayan gurfanar da wadanda ake zargin a babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai shari’a, Justice Nasiru Saminu.

An zaman kotun na ranar laraba an gabatar da mutane hudu kan tuhumar da ake yi musu na zargin kisan kan wata yarinya mai suna Hafsat Auwal tare da kwakwulu mata ido, wadanda dukkansu suka musanta zargin.

A tuhumar zargin kisan kan matar ,Fatima Abubakar da yayan ta shida, wanda ke tuhuma na farko ya amsa laifin yayin da sauran suka musanta.

Haka zalika sakamakon rashin lauyan da zai kare su a zargin halaka wasu matan aure, a unguwar Tudun Yola Kano, kotun ta sanya ranar 20 ga watan Afrilu don karanta musu tuhumar.

Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa ya hada da zargin hada kai da fyade da kisan kai da fashi.

Alkalin kotun mai shari justice Nasiru Saminu ya bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali da tarbiya.

A karshe lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista S.M. Tahir ya ce duk bayanan da suka fadawa yan sanda suna hannunsu kuma za su gabatar da ingantattun shaidun don tabbatar da laifin da ake yi musu.

Post masu alaƙa

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar ADC

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi – Baba Jibo

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta raba Naira miliyan ɗaya ga matasa 36 a shirin haɗin gwiwa na magance aikata laifuka