Mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya mai kula da shiya ta ɗaya dake Kano, AIG Garba Ahmed, ya bai wa iyalan ƴan sandan da suka rasu tallafin kuɗi naira miliyan tara da dubu ɗari biyu da 260 da kobo 88 ( ₦9,260,204.88).
Mai Magana yawun rundunar shiya ta ɗaya, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce wannan na cikin ƙudirin rundunar ƴan sanda ta ƙasa, bisa jagorancin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, na ci gaba da sanya farin ciki da walwala ga iyalansu.
DSP Abdullahi Hussaini, ya ƙara da cewa an bayar da tallafin ne a ci gaba da gudanar da bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026.
Waɗanda suka samu tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da yin alƙawarin za su yi amfani dashi ta hanyar data dace.