Rundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar da Nasarar Halaka ‘Yan Boko Haram 63

Hedikwatar rundunar tsaro ta sojin Nijeriya, ta bayyana cewa, dakarunta sun yi nasarar halaka ‘yan ta’addar Boko Haram 63 tsakanin farkon watan Maris zuwa 15 ga watan Afrilu.

Baya ga kashe ‘yan ta’addan, sojojin sun kuma ceto sama da mutane 150 da aka sace, a yayin gudanar da ayyuka daban-daban a wasu yankunan kasar nan.

Manjo Janar Musa Danmadani, Daraktan yada labarai na tsaro, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar tsaro, cewa sojojin da suke aikin sun kuma kwato kayayyaki da dama da suka hada da bindigogi 36 ak-47, AK-47, da sauran manyan makamai.

Sauran sun hada da kayan abinci, babura, abubuwan fashewa shanu daga hannun ‘yan ta’addar.

Ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato danyen mai na sata da kuma gas na mota wanda kudinsu ya kai naira miliyan N259m daga hannun tsagerun yankin Neja Delta.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr