Rundunar Yan Sandan Jigawa Ta Bayyana Nasarar Data Samu Bayan Kashe Masu Garkuwa Da Mutane

Daga: Bashari Auwal

Rundunar Yan’sandan jiha Jigawa ta samu gagarumar nasara a kokarinta na hana aikata manyan laifuka da kanana tare da tabbatar da bin doka da Oda a fadin jihar.

Kwamishinan Yan’sandan jihar CP AT Abdullahi ne ya sanarda haka ga yan’ jaridu a ranar Larabar nan a Harabar Shelkwatar dake Dutse.

AT ya ce sakamakon ayyaukan hadin gwiwa tsakanin Yan’sandan Kananan Hukumomi na Gumel da Gagarawa, Garki da Ringim, Sule Tankarkar da taimakon Yan ‘ Bijilanti da maharba da kuma ‘yan Bulala sun kubutar da wata Dattijuwa yar’ kimanin shekara 80 Mai suna Hajiya Hajara wadda wasu masu garkuwa da mutane suka dauko ta daga wani kauyen bisa Babura a karamar Hukumar Minjibir su kimanin 12 inda suka rinka kara-kaina da ita tsakanin kauyukan Danzomo da Medi a karamar Hukumar Sule Tankarkar.

Kwamishinan yace da samun labari, nan da nan jami’an da sauran abokan aiki suka garzaya maboyar ta su inda suka yi musayar wuta.Amma a karshe, sun samu nasarar hallaka biyar daga cikin masu garkuwar yayin da sauran suka samu raunuka.

Kazalika, Rundunar ta cika hannu da jagoran ‘masu garkuwar garkuwar mai suna Yahya mai shekara 35 dake kauyen Katoren Fulani a karamar Hukumar Garki. A cewar Kwamashinan, an kai matar da aka yi garkuwar da ita Asibiti inda aka tabbatar tana cikin koshin lafiya. Rundunar Yan’sandan ta kuma kwace wasu makamai da suka hadar da Bindiga kirar AK-47 guda daya da wata bindigar wadda ke sarrafa kanta da albarusai 14 sai kuma wayoyin tafi da gidanka guda 3.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto