Sabon kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da aiyuka na musamman na jihar Kano, Air Commodore Salisu Yusha’u (mai ritaya), ya tabbatar da aniyarsa ta haɗa kai da rundunar ’yan sanda domin ƙarfafa tsaro a jihar.
mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ga kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, a hedikwatar rundunar da ke Bompai ranar Alhamis.
Air Commodore Yusha’u ya yaba da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da alƙawarin cewa ma’aikatarsa za ta ba ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da aiyukansu.
Ya kuma yi ta’aziyyar rasuwar jami’an ’yan sanda da suka mutu a bakin aiki a yankin Sokoto da Zamfara, da kuma rasuwar SP Salisu Wakili, yana mai cewa rasuwarsu babban rashi ne ga rundunar da jihar Kano.
A nasa jawabin, kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana ziyarar a matsayin wata alama ta kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da sauran al’umma da su guji kalaman ƙiyayya, musamman a wannan lokacin da ake tunkarar harkokin zaɓe, tare da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimaka musu wajen dakile laifuka.
Kwamishinan ’yan sandan ya jaddada cewa tabbatar da tsaro nauyi ne na kowa, yana mai cewa al’umma da ’yan sanda ba za su iya rabuwa da juna ba.