Sabon Gwamnan Kano Ya Shawarci Masu Gine Filayen Gwamnati da Su Dakata

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayar da Shawara ga dai daikon  Jama’a da kungiyoyi da suke ci gaba da gine-gine a filaye mallakar gwamnati ciki da kewayen kano  da suka hada da dukkanin Makarantu na Jiha da dukkan wuraren Addini mallakin jihar da asibitoci da makabartu da kuma kwaryar birnin Kano.

Zababben gwamnan ya yi mika wannan shawarar ta hannun kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a ranar Alhamis.

Idan za a iya tunawa tun gabanin zaben gwamnan Kano yayin yakin Neman zaben gwamnan an jiyo Jagoran Jam’iyyar Sanata Rabi’u Kwankwaso na ikirarin rushe irin wadannan wuraren da gwamnatin Jihar mai ci ta gwamna Ganduje ta cefanar da su.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.