Zababben Gwamnan Kano Ya Naɗa Sakataren Yada labaransa

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Sanusi Bature Dawakin Tofa a matsayin sakataren yada labaransa zuwa lokacin karbar mulki.

A wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Alhamis, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin karbar mulki, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana Sanusi Bature a matsayin jajirttace kuma wanda yasan aikinsa.

Sanusi, wanda a baya ya yi aiki a bangarori da dama kama daga kungiyoyin cikin gida da na kasashen waje, shi ne mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar NNPP a zaben gwamna da aka kammala a jihar.

A ranar Laraba ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Jihar Kano ta bai wa zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf takardar shaidar lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga wannan watan Maris.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.