Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa matsalolin tsaro a Sokoto – Aliyu

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa kusan kashi 80 na matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Aliyu ya ce mafi yawan masu aikata laifuka a jihar da ƴanbindiga na amfani da miyagun ƙwayoyi kafin su aikata ta’addanci.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Idris Mohammed Gobir, ya wakilta ya bayyana hakan ne a yayin wani taron lacca da aka shirya domin tunawa da ranar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu.

“Kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaron da ke addabar jiharmu suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi. Waɗannan mutane na amfani da ƙwayoyi masu haɗari. Mutumin da yake cikin hankalinsa ba zai dubi wani ɗan adam ya kashe shi ba,” in ji shi.

Aliyu ya kuma buƙaci matasa su guji shiga harkar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi domin samun damar zama shugabanni da fitattun mutane a nan gaba.

Ya ce gwamnatin jihar ta kafa ofishin babban mataimaki na musamman kan daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi domin jagorantar shirye-shiryen wayar da kan jama’a.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi Bitar Albashi Mafi Ƙaranci Na N70,000 — Gbajabiamila

Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isah Umar ya yaba da ƙoƙarin ƴan sandan Kano wajen daƙile laifuka.

Gwamnatin Oyo ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 10