Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta yi bitar mafi ƙarancin albashin na Naira 70,000 da aka ƙayyade a shekarar 2024.
Ya bayyana hakan ne a wani taron da ƙungiyar Working People United (WoPU) ta shirya a Abuja, inda ya ce albashin Naira 70,000 ba ya iya biyan buƙatun ma’aikata la’akari da yanayin tattalin arziki da aka tsinci kai a halin yanzu.
A cewarsa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rage wa’adin sake nazarin mafi ƙarancin albashi daga shekara biyar zuwa shekara uku domin ya riƙa tafiya da sauye-sauyen tattalin arziki.
Gbajabiamila ya ce gwamnati za ta tattauna da ƙungiyoyin ƙwadago wajen duba batun albashin
Shi ma Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Dingyadi, ya ce manufofin gwamnati ba za su amfani ma’aikata ba sai an aiwatar da su yadda ya kamata.