Shugaba Muhammadu Buhari Mutum Ne Mai Gaskiya Da Zabin Cancanta : Muhammad Babandede,OFR, OCM

Tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Muhammad Banbandede, OFR ,OCM, ya bayyana rasuwar tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin babban rashin da za a dade, ba a manta da dashi ba.

A cewarsa, Marigayi Muhammadu Buhari, mutum ne mai son gaskiya da zabin wadanda suka cancanta kafin ya basu wani jagoranci, kuma idan ya basu ya basu ne tsakani da Allah domin yasan za su iya rike amanar da ya su.

Muhammad Babandede, ya bayyana hakan ne lokacin da ake tattaunawa dashi kai tsaye ta manhajar ZOOM, a cikin shirin Ina Kwana na gidan Telebijin da Radiyo na Muhasa, a ranar Litinin.

Tsohon shugaban hukumar, ya fara da yin ta’aziyarsa ga iyalan marigayi Muhammadu Buhari da makusantansa,musamman Mamman Daura, inda ya ce tsohon shugaban kasar mutum ne mai bin doka da oda tare da jajircewa kan gaskiya komai ɗacin ta.

Ya ƙara da cewa ko lokacin da aka rufe Boda don hana shigo da kaya, akwai damuwa a kasar, amma jama’a basu sani, inda gwamnatin Muhammadu Buhari, ta yi shawara don rufe bodar kuma ba a hana mutane shigowa ba’.

‘’ Ina so na fada muku lokacin da aka rufe Boda akwai damuwa ne,ina son gaya muku akwai damuwa ne mutane basu fahimta cewa ba, kasa kamar Benin kasa ce wadda kullum tana duba abinda Nijeriya take ciki kafin ta sake batashi, idan Nijeriya ta ce a shigo da mota, a biya harajin Kwastam Naira dubu biyar to ita Benin sai ta Naira dubu uku ko kasa da haka, to kaga ai za su kawo nan sai a shigo da kaya ta hanyar fasa kwauri ta Boda’’.

‘’Saboda haka gwamnatin Buhari, ta yi shawara ta rufe Boda, amma a ranar da aka rufe boda , bayan kwana biyu zuwa uku na sami shugaba Muhammadu Buhari, kuma na rubuta masa a rubuce , cewar in za a tare kaya to a bar mutane su shiga, inaso in sanarwa jama’a in mun hana kaya su shiga, to mun bar mutane su shiga kaga wannan ra’ayin shi ne na Buhari amma da na yi masa magana sai ya yadda’’.

Ya kuma ce lokacin Buhari ya basu dama a matsayinsu na ma’aikata musamman wajen fadar ra’ayinsu ba tare da tursasawa ba.

‘’Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai karɓar shawara, domin yana amincewa jama’a su faɗi ra’ayinsu ba tare da tursasawa kowa ba’’ Muhammad Babandede’’. Haka zalika ya bayyana nasarorin da aka samu lokacin da yake riƙe da shugabancin hukumar shige da fice ta ƙasa, bisa cikakken goyon bayan da tsohon shugaban ƙasar ya basu.

A karshe ya kwatantsashi da shugaba adali wanda bai yadda da rashin gaskiya ba.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda