Home » Shugaba Tinubu Ya Jinjina Wa Haƙuri Da Juriyar ‘Yan Najeriya 

Shugaba Tinubu Ya Jinjina Wa Haƙuri Da Juriyar ‘Yan Najeriya 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jinjinawa wa ’yan Najeriya ya kuma tabbatar musu da cewa sadaukarwarsu za ta haifar da sakamako mai tasirin gaske nan ba da jimawa ba.

Shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin gabatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 ga majalisun dokoki ƙasa.

Ya bayyana amincewarsa da cewar watanni 18 na gwamnatinsa sun kasance masu wuya matuƙa.

Sai dai ya roƙi ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin haƙuri.

“Aikin bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaba, wanda muka fara watanni 18 da suka gabata a matsayin ƙasa, yana ci gaba da tafiya,” in ji shi.

“Babu wata hanya da ta dace mu zaɓa, hanya ɗaya ce da dole muka ɗauka domin Najeriya ta samu damar zuwa wani babban mataki.

 

“Na gode wa kowane ɗan Nijeriya da yake tafiya tare da mu a wannan tafiya ta gyara.”

 

Ya ƙara da cewa, “Hanyar gyaran a yanzu tana samar da kyakkyawan sakamako sosai, kuma a matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, na san cewa wannan hanya ba ta kasance mai sauƙi ba.

 

“An sha wahalhalu. Kuma hakan ba zai tafi da banza ba. Dole ne mu ci gaba da amincewa da tsarin domin cikar burinmu.”

 

Kasafin kuɗi na 2025, kamar yadda Tinubu ya bayyana, na nufin ɗorawa kan ayyukan da gwamnatinsa ta faro watanni 18 da suka gabata.

Har ila yau, ya ce gwamnatin za ta mayar da hankali kan sake tsara hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi, ilimi, bunƙasa kasuwanci da sauransu.

Ya sake jaddada burinsa na ganin tattalin arzikin Najeriya, ya bunƙasa tare da yin gogayya da manyan ƙasashen duniya.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?