Shugaban ƙasar Najeriya ya dakatar da shugaban hukumar EFCC

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da yi wa Tattalin Ariƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya ta ce shugaban ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ke kan Bawa.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ta ce an bai wa AbdulRasheed Bawa umarnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa za ta haɗa gwiwa da Masar kan noman dabino da dankali

Yar Gombe ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta duniya a Saudiyya

Miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum 80 a Kano