Hukumar DSS Ta Fara Binciken Dakataccen Shugaban EFCC, Abdurrasheed Bawa

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa (DSS) ta gayyaci dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annanti  ta EFCC, Abdurrasheed Bawa domin amsa tambayoyi bayan da shugaba Tinubu ya dakatr da shi a yammacin jiya.

Bawa ya isa hedikwatar hukumar ta DSS da ke Abuja ‘don amsa gayyatar da aka yi masa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mista Peter Afunanya shi  ya tabbatar da gayyatar da aka yi wa Bawa, ya kuma jaddada cewa, yana daga cikin hanyoyin gudanar da bincike kan dimbin zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa Bawa.

Wannan lamari na zuwa ne  ‘yan sa’o’i kalilan bayan da Shugaban kasa  Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa na shugaban hukumar ta yaki da ta’annanti ta (EFCC).

A bisa umarnin shugaba Tinubu, an umurci Bawa ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar.

Wannan tsari zai bada damar ci gaba da aiki a ofishin shugaban hukumar har sai an kammala bincike.

Hukumar ta  EFCC dai, tana taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun kudaden kasa da kuma tabbatar da cewa an magance laifukan tattalin arziki yadda ya kamata.

Post masu alaƙa

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci