Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi shugabannin jam’iyyun siyasa da ’yan takara da su guji tashin hankali, kalaman kiyayya da yada labaran karya gabanin babban zaben 2027.
Kwamishinan ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa da ’yan takara a Kano.
Ya bukace su da su tabbatar da cewa magoya bayansu sun bi doka, tare da mutunta dokar zabe ta 2022 da ka’idojin hukumar zabe ta kasa, INEC.
Wakilin INEC da kuma wakilan jam’iyyun siyasa 13 sun halarci taron, inda suka yi bayani tare da bayyana goyon bayansu ga kokarin rundunar na tabbatar da zaman lafiya.
Kwamishinan ya ce rundunar ’yan sanda, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za ta samar da isasshen tsaro a wuraren zabe, da wuraren yakin neman zabe.
Ya ce za a kuma kara tattara bayanan sirri tare da kafa cibiyar kula da tsaron zabe da kuma wurin karbar korafe-korafe.
Ibrahim Bakori ya gargadi duk wanda ya karya doka ko ya aikata laifin zabe cewa za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da su sanya zaman lafiya a gaba, yana mai cewa Kano za ta iya zama abin koyi wajen gudanar da zabe cikin lumana.