Home » Shugaban Kasar Najeriya Ya Amince da Nadin Hafsoshin Sojin Kasar da Mashawarci Kan Tsaro

Shugaban Kasar Najeriya Ya Amince da Nadin Hafsoshin Sojin Kasar da Mashawarci Kan Tsaro

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yi wa dukkan hafsoshin tsaron Nijeriya da sufeto-Janar na ‘yan sanda da masu ba da shawara kan sha’anin tsaro da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam murabus daga Ma’aikatunsu tare da maye gurbinsu nan take.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yi wa dukkan hafsoshin tsaron Nijeriya da sufeto-Janar na ‘yan sanda da masu ba da shawara kan sha’anin tsaro da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam murabus daga Ma’aikatunsu tare da maye gurbinsu nan take.

Hafsan hafsoshin sun hada da babban hafsan tsaro, Lucky Irabor da babban hafsan soji, Farouk Yahaya da Shugaban Hafsan Sojin Ruwa, Awwal Gambo sai shugaban hafsan sojin sama, Isiaka Amao da kuma Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alkali.
A cewar sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, sabbin jami’an da aka nada su ne:
 Mallam Nuhu Ribadu a matsayin babban mai ba da shawara kan sha’anin tsaron Nijeriya.
Sauran sun hada da “Maj. Janar C.G Musa a matsatyin Shugaban Hafsan Tsaro, da Maj. T. A Lagbaja a matsayin Babbab Hafsan Sojojin Nijeriya. Da Rear Admirral E. A Ogalla a matsayin Shugaban hafson sojojin ruwa,
Sai AVM H.B Abubakar Shugaban Hafsan Sojan Sama sai DIG Kayode Egbetokun Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda.
Sai kuma Maj. Janar EPA Undiandeye, matsayin shugaban hukumar leken asiri na kasa

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi