Shugaban Najeriya Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Sarkin Morocco

Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarkin Morocco Mohammed na 6, bayan mummunar girgizar kasa da ta afku a kasar a ranar Asabar, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Shugaban ya jajanta wa dukkan iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu da duk wadanda bala’in ya shafa, tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa.

Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya tabbatar wa gwamnatin da al’ummar kasar Maroko cewa, ‘yan Nijeriya na tare da su a wannan mawuyacin hali na jarrabawa da alhini da kasar ke ciki, kuma suna yi musu addu’ar Allah ya yaye musu.

A jiya ne dai Sarkin Muhammad na shida ya ayyana zaman makokin kwana uku a faɗin ƙasar.

Ya kuma bayar da umarnin kai taimakon tanti da abinci da sauran kayan agaji ga waɗanda suka tsira – sannan ya tura sojoji domin su taimaka wajen aikin ceto da ake ci gaba da yi.

Sannan an sauke tutocin ƙasar zuwa rabi a kusan duka gine-ginen ƙasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya rawaito.

Post masu alaƙa

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kwace kadarorin Godwin Emefiele

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China