Wata Kotun Majistare da ke Nomansland a Ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu kan zargin satar gwala-gwalai da kuɗi da kuma wayar salula.
Masu laifin da ake tuhuma su ne Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini. An gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumar haɗin baki, sata da kuma karɓar kayan sata.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Barista Abubakar Ibrahim, ya shaida wa kotu cewa Sulaiman Yakubu, wanda shi ne direban matar Sarki Sanusi II, ya shiga ɗakinta ba bisa ƙa’ida ba, ya kwashe gwala-gwalai da darajarsu ta kai Naira miliyan 60, tare da kuɗi da kuma wayar salula.Lokacin da aka karanta tuhumar, Sulaiman ya amsa laifin, amma sauran biyun suka ce ba su aikata ba.
Lauyansu, Barrista A.A. Abdullahi, ya nemi kotu ta ba su beli.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Halilu Abdurahman ya amince da belin tare da sharuɗɗa, ciki har da samar da mai tsaya musu, wanda zai kasance uba ko ɗan’uwa, kuma ma’aikacin gwamnati da ba zai gaza matakin albashi na 15 ba, tare da biyan Naira miliyan 10 kowanne.
Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu don ci gaba da sauraro, yayin da aka tsare su har sai sun cika sharuɗɗan belin.
AMINIYA