Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sanar da naɗin CP Umar Ahmed Chuso a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan jihar.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Babban Sufeton ’Yan Sanda (IGP) ne, ya tura CP Chuso zuwa Gombe.
Tuni ya fara aiki a matsayin Kwamishinan ’Yan Sanda na 24 a jihar.
Sanarwar ta ce sabon kwamishinan ya karɓi muƙamin ne a lokacin da rundunar ke ƙoƙarin ƙara inganta tsaro da yin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da al’ummar jihar.
CP Chuso, gogaggen jami’in ’yan sanda ne da ke da ƙwarewa a harkar tsaro.
- Hukumar PSC ta ɗaga likafar AIG Muhammad Usaini Gumel zuwa DIG.
- Hukumar NOA da rundunar sojoji sun ƙudiri aniyar haɗa kan jama’a da kuma sanya kishin ƙasa.
Ana sa ran zai ci gaba da kula da tsaro, tare da kawo sabbin hanyoyi da za su taimaka wajen hana aikata laifuka, amfani da bayanan sirri, da kusantar da ’yan sanda ga jama’a.
Rundunar ta buƙaci al’ummar Jihar Gombe da su bai wa ’yan sanda haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai masu muhimmanci a kan lokaci domin tabbatar da tsaro.
Ta kuma tabbatar wa jama’a cewa sabon Kwamishinan ya ƙudiri aniyar yin aiki da gaskiya, ƙwarewa da amana, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Rundunar ’yan sandan ta ƙara da cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Gombe.