Dakarun Sojin Najeriya sun ceto wasu mutane huɗu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram, sun yi garkuwa da su tare da tsare su na tsawon shekaru uku a Jihar Borno.
Sojojin sun ceto su ne da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar 21 ga watan Agusta, yayin wani samame da suka kai kusa da ƙauyen Kauwa, da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa.
Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri kan wasu ‘yan ta’adda da ake zargin sun tsere daga yankin.
Kwamandan rundunar, Laftanar Kanar E.E. Ukhun ne, ya jagoranci aikin.
A lokacin da sojojin suka yi wa mutanen tambayoyi, sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun sace su ne daga Ƙaramar Hukumar Mafa kimanin shekaru uku da suka gabata.
Sun ce daga Mafa aka kai su sansanin ‘yan ta’adda da ake kira Dogon Chuku, inda aka tsare su har zuwa lokacin da sojoji suka ceto su.
Bayan ceto su, sojojin sun bai wa mutanen abinci sannan suka fara tantance su.
A halin yanzu, ana kula da lafiyarsu a cibiyar kiwon lafiya ta rundunar sojoji ta 19, kafin daga bisani a kai su hedikwatar Operation Hadin Kai domin ci gaba da yi musu tambayoyi.
Rundunar ta ce aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da sojojin Operation Hadin Kai da rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ke yi a kusa da Tafkin Chadi.
Ta ce sojojin na kuma amfani da bayanan sirri domin gano wuraren da ‘yan ta’adda ke ɓoye da kuma daƙile ayyukansu a yankin.
Majiyoyin tsaro sun ce za a ci gaba da yi wa mutanen da aka ceto tambayoyi domin samun ƙarin bayani kan yadda aka yi garkuwa da su da kuma ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.