• Home  
  • Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta’adda 80 A Katsina
- Labarai

Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta’adda 80 A Katsina

‘Yan ta’adda sun jima suna addabar yankuna da dama a jihar Katsina, duk da irin ƙoƙarin da gwamnatoci ke iƙirarin yi.

Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta halaka sama da ƴan ta’adda 80, a wani ƙauyen jihar Katsina. 

Ta ce ta yi nasarar ƙone baburansu 45 sakamakon luguden wutar da ta yi musu a daren ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar a ranar Litinin.

Sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarun rundunar sojin, Edward Gabkwet ya sanyawa hannu, ta ce an kai harin ne a wata maɓoyar ƴan bindigar da ke ƙauyen Gidan Kare a ƙaramar hukumar Faskari.

Sanarwa sojojin ta ce ta kai harin ne a daren ranar Asabar a lokacin da ta samu rahoton cewa ƴan ta’adda kimanin 100 sun kai hari a wani ƙauyen da ke da nisan kilomita biyar daga Gidan Kare, inda suka ƙone gidajen jama’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai