Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 5 A Borno

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.

Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka yi musayar wata da su suka fatattaki maharan da hadin gwiwar dakarun rundunar ta 134 da suka isa garin.

A yayin arangamar ’yan ta’addan sun tsere sun bar nau’uka daban-daban na makamai da suka hada da kuma na’urar sadarwa.

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ta’addanci, musamman bisa la’akari da yawaitar hare-haren ’yan ta’addan da suka zafafa a kwanan nan a yankin Arewa Maso Gabasa

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.