• Home  
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 5 A Borno
- Babban Labari - Labarai

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 5 A Borno

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar […]

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.

Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka yi musayar wata da su suka fatattaki maharan da hadin gwiwar dakarun rundunar ta 134 da suka isa garin.

A yayin arangamar ’yan ta’addan sun tsere sun bar nau’uka daban-daban na makamai da suka hada da kuma na’urar sadarwa.

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ta’addanci, musamman bisa la’akari da yawaitar hare-haren ’yan ta’addan da suka zafafa a kwanan nan a yankin Arewa Maso Gabasa

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai