Sojojin Najeriya sun ceto wani fasto daga hannun ƴanbindiga a Enugu

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta tare da haɗin gwiwar ƴan sa kai ta JTF da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar ceto wani fasto da aka sace, Reverend Johnson Anayo Onugwu, a jihar Enugu.

An sace faston ne daga gidansa dake al’ummar Ezimo, ƙaramar hukumar Udenu, a daren 29 ga Janairu 2026 da misalin karfe 1:00 na dare, yayin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye gidansa.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce sojojin da ke garin Udenu sun bi sawun masu garkuwa da fasto ɗin ne bisa bayanan sirri da suka samu inda daga bisani suka yi musayar wuta da ƴanbindigar a al’ummar Okpakeke da ke yankin Itabolo.

Musayar wutar tsakanin sojojin da ƴanbindigar ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga ƴanbindigar lamarin da ya bai wa sojoji damar ceto faston cikin nasara.

Sanarwa ta kuma ce sojojin sun samu nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da mujallu da harsasa.

Rundunar ta bayyana cewa, za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda