APC

Tsohon Shugaban ’Yan Sanda ya janye daga takarar Gwamnan Yobe

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alƙali, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar Gwamnan Jihar Yobe. Usman Baba Alƙali wanda ke neman takarar Gwamnan Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, ya sanar da haka ne ta wata takardar sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa ne […]

Read more

Abba kaɗai ke da takarar kai-tsaye a Kano —APC

Jam’iyyar APC ta saya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano fom ɗin neman tazarce babu hamayya a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Shugabannin Jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bayan sun rungumi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba a matsayin ’yan takara babu hamayya a kujerar shugaban ƙasa da […]

Read more

Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe

A wani gagarumin sauyin siyasa a Jihar Yobe, ƙungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Potiskum.   Sauyin sheƙar wanda shi ne mafi girma a yankin a ’yan kwanakin nan ya samu jagorancin Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da Soja Boy. Masu […]

Read more

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom sun yi watsi da shirin baiwa ɗan takara tikitin kai tsaye domin kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Ikot Ekpene/Obot Akara, gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda suka bayyana hakan a matsayin saɓawa ka’idojin dimokuraɗiyya. An bayyana matsayar ne […]

Read more

Ko Amupitan ya sauka ko mu ɗauki matakin ban mamaki – ADC

Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya tace ko Shugaban Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta INEC Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa ko kuma sau ɗauki matakin da zai girgiza kasar. Jam’iyyar ta bayyana haka ne lokacin da take gabatar da wasu sabbin zarge-zarge kan shugaban hukumar. ADC ta soki Amupitan kan tsofaffin bayanansa da […]

Read more

Dan Sarkin Daura ya fito takarar dan Majalisar Wakilai

Muhammad Daha, ɗa ga Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Baure/Zango a zaɓen 2027. Daha, wanda ke rike da sarautar Danburam na Daura, ya ce matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye  daga al’ummarsa da ke son ya wakilce su a Majalisar Tarayya. “Ina […]

Read more

Ƴan majalisar wakilai 8 na Kano sun fice daga NNPP zuwa APC

Ƴan Majalisar Wakilai takwas daga Jihar Kano sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar NPP zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar jihar. Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya sheƙar a hukumance yayin zaman majalisar a yau Talata, bayan karanta wasiƙun da ‘yan majalisar suka aike wa zauren. A cikin […]

Read more