Sunayen sabbin shugabannin jam’iyar APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorance har an da shekaru huɗu masu zuwa.

An zaɓi sabbin shugabbnin ne a lokacin babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.

APC ta sanar da zaɓen Farfesa Nentawe Yilwatda – shugaban riƙon jam’iyyar – a matsayin cikakken shugabanta na ƙasa.

Haka kuma jam’iyyar ta tabbatar da Surajudeen Basiru a matsayin cikakken sakataren jam’iyyar na ƙasa.

An dai zaɓi mafi yawan jagororin jam’iyyar ta hanyar masalaha, kamar yadda jam’iyyar ta fi bai wa fifiko.

Ga jerin sunayen sabbin jagororin jam’iyyar:

  • Shugaban Jam’iyya na ƙasa: Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Mataimakin Shugaba (Arewa): Ali Bukar Dalori
  • Mataimakin Shugaba (Kudu): Dr. Benjamin Obi Nwoye
  • Sakataren Jam’iyyar na ƙasa: Sen. Surajudeen Ajibola Basiru
  • Mataimakin Sakatare: Prof. AbdulKarim Abubakar Kana
  • Babban Lauyan Jam’iyya: Murtala Aliyu Kankia
  • Babban Ma’aji na ƙasa: Uguru Mathew Ofoke
  • Babban Sakataren Kuɗi: Amb. Haruna Ginsau
  • Babban Sakataren tsare-tsare: Muhammad Sulaiman Argungu, OFR
  • Sakataren Walwawa: Donatus Enyinnah Nwankpa
  • Sakataren Yaɗa Labarai: Felix Morka
  • Babban Mai Binciken kuɗi: Sen. Abubakar Maikafi
  • Shugabar Mata: Dr Mary A. Idele
  • Shugaban Matasa: Dayo Israel

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda