Tag: APC

Babban Labari Labarai

Abin da ya sa na koma APC – Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma shari’o’in da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne babban dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar zuwa APC. A ranar Litinin ne gwamnan ya sanar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance bayan wani […]

Babban Labari Labarai

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance. A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha a ranar Juma’a, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito. Sauya shekar […]

Babban Labari Labarai

Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa jihar Kano domin karɓar gwamnan Abba zuwa jam’iyyar APC, a wani muhimmin taron siyasa da ya ja hankalin jama’a. An shirya taron karɓar gwamnan ne a hukumance a filin wasan Sani Abacha Stadium, inda dubban magoya baya da shugabannin jam’iyya suka fara taruwa tun da wuri. Rahotanni sun […]

Babban Labari Labarai

Babandede Ya Sabunta Rajistarsa A APC, Ya Samu Gagarumar Tarba.

Tsohon Shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya sabunta rajistar zamansa ɗan jam’iyyar APC a Hadejia, Jihar Jigawa. Babandede ya samu gagarumar tarba daga dimbin magoya baya da suka tarbe shi, daga ƙofar gari har zuwa mazabarsa ta Kasuwar Ƙuda, tafiyar mintuna kaɗan ce, amma ta ɗauki sama da awa […]

Babban Labari Labarai

Atiku ya buƙaci Inec ta sauya lokacin zaɓen 2027

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta da ta gaggauta sake duba ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaɓe na 2027, yana mai cewa lokacin ya yi karo da azumin watan Ramadan. A ranar Juma’a INEC ta sanar cewa za a gudanar da zaɓen shugaban […]

Babban Labari Siyasa

APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano

Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf. An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar. Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da […]

Labarai Siyasa

APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam’iyyar ta saka ranakun 27 […]

Babban Labari Labarai

Ba mu da shirin sauke Sarki Sanusi II — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kan mulki bayan sauya sheƙar gwamnan daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki. Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya kan lamarin […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai