Tag: APC

Babban Labari Labarai

Atiku ya buƙaci Inec ta sauya lokacin zaɓen 2027

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta da ta gaggauta sake duba ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaɓe na 2027, yana mai cewa lokacin ya yi karo da azumin watan Ramadan. A ranar Juma’a INEC ta sanar cewa za a gudanar da zaɓen shugaban […]

Babban Labari Siyasa

APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano

Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf. An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar. Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da […]

Labarai Siyasa

APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam’iyyar ta saka ranakun 27 […]

Babban Labari Labarai

Ba mu da shirin sauke Sarki Sanusi II — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kan mulki bayan sauya sheƙar gwamnan daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki. Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya kan lamarin […]

Babban Labari Siyasa

Kwankwaso ya karyata rahotan Premium Times na cewa ya goyi bayan gwamnan Kano zuwa APC

Jagoran jam’iyyar NNPP, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta wani rahoto na jaridar Premium Times da ke cewa ya goyi bayan shirin sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC. Wannan na cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Saifullahi Hassan, ya fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce […]

Babban Labari Siyasa

An jibge motocin yaƙi a Gidan Gwamnatin Kano

An tsaurara ƙarin jami’an tsaro a gidan Gwamnatin Jihar Kano a safiyar Litinin a yayin da ake dakon sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf. Wakilinmu ya lura cewa an girke ƙarin ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS a babbar ƙofar shiga da wasu muhimman wurare a gidan gwamnatin. Sojoji sun ceto fasinjojin da […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai