Gwamnatin Yobe ta ware kimanin Naira miliyan 398 domin shirin ciyar da masu azumi da kuma gudanar da tafsirin watan Ramadan na shekarar 2026 a faɗin jihar.
Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayar da wannan tabbaci, wanda ya ce shirin zai gudana ne a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Addini da Sake Fasalta Ɗabi’a ta jihar, da nufin tallafa wa al’umma, musamman marasa galihu, a cikin watan Ramadan mai alfarma.
Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Buni ya amince da faɗaɗa shirin ta hanyar ƙara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 101 da aka yi amfani da su a bara zuwa cibiyoyi 130, waɗanda aka baza a dukkan ƙananan hukumomi 17 na jihar.
Ana sa ran kowace cibiya za ta riƙa samar da abincin buɗa-baki wa mutane 100 a kowace rana tsawon watan azumi.
A bayanin da gwamnatin ta fitar, sama da Naira miliyan 338 za a kashe wajen sayen raguna da kayan miya da sauran kayan girki domin sauƙaƙa gudanar da ciyarwar a cibiyoyin da aka tanada.
Baya ga haka, an ware Naira miliyan 60 domin biyan alawus ga malaman addinin Musulunci da za su jagoranci tafsiri, tare da bayar da wa’azi da koyarwa don ƙara kusantar da al’umma da Allah (SWT) a wannan wata mai falala.
A ɓangaren ƙara ƙarfafa shirin, Gwamna Buni ya kuma amince da rarraba buhunan shinkafa 2,300 da jerkokin man girki 400 a cibiyoyin ciyarwa 130 da ke faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen bikin rarraba kayan, Kwamishinan Harkokin Addini da Sake Fasalta Ɗabi’a na Jihar Yobe, Alhaji Yusuf Umar (Kaigaman Potiskum), ya yaba wa gwamnan bisa ci gaba da faɗaɗa shirin ciyar da masu azumi, yana mai bayyana hakan a matsayin hujja ta jajircewar gwamnati wajen kula da walwalar marasa galihu.
Ya jaddada cewa shirin wanda aka daɗe ana aiwatar da shi, ya kasance wani gagarumin tallafi ga iyalai da dama a faɗin jihar, musamman a lokacin Ramadan.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga mambobin kwamitocin da ke kula da cibiyoyin ciyarwa da su yi aiki da gaskiya da amana, tare da kauce wa duk wani yunƙurin karkatar da kayan tallafin.
Ya yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani rashin ɗa’a ko saɓa ƙa’idojin shirin ba, yana mai umurtar dukkan jami’an da ke da hannu a aiwatar da shirin da su bi dokoki da ƙa’idoji domin tabbatar da nasarar shirin gaba ɗaya.
Shirin na Ramadan na bana, a cewar gwamnati, wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na tallafa wa al’umma, ƙarfafa haɗin kai, da kuma bunƙasa ibada a cikin watan Ramadan mai alfarma.