Muna Buƙatar Masu Fassara A Asibitoci : Kurame

Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe.

Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari.

Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki.

Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum gare su.

“Matsalarmu ba kiwon lafiya kaɗai ta shafa ba, a fannin ilimi, akwai makaranta ta musamman a faɗin jihar nan, kuma an bar yaranmu da dama a baya. Muna buƙatar ingantacciyar makarantar sakandaren kurame a jihar,” in ji shi.

Abba ya kuma yi kira da a sanya masu fassara a cikin shirye-shiryen gwamnati da kuma taron jama’a, don tabbatar da cewa bayanai kan manufofi da dama sun isa ga kurame.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta tallafa wa mambobin ƙungiyar da jarin fara aiki, yana mai jaddada cewa da yawancinsu suna son yin kasuwanci amma ba su da hali.

Baba Kucici, sakataren ƙungiyoyin fararen hula a Jihar Yobe, shi ma ya gabatar da jerin tarin bukatun ’yan kasa a wurin taron.

Ya jaddada bukatar gwamnati ta samar da hanyar da za ta riƙa bibiyar ayyuka da shirye-shirye kai tsaye, yana mai cewa hakan zai nuna ɗaukar nauyi da kuma samun amincewar jama’a.

Aminiya ta ruwaito cewa tattaunawar ta tattaro masu ruwa da tsaki daga gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, da ƙungiyoyin al’umma don daidaita abubuwan da ’yan qasa suka sa a gaba kafin kasafin 2026

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda