Za A Samu Sabbin Masu Kamuwa Da HIV Miliyan Shida Nan Da 2029 – MDD

Shirin Majalisar Dinkin Duniya kan cutar sida ko HIV/AIDS ya yi hasashen samun ƙarin masu kamuwa da cutar miliyan shida – da kuma mutuwar mutum miliyan hudu – nan da shekarar 2029 sakamakon katsen tallafin da Amurka ke bayarwa kan yaƙi da cutar.

A yau ne ake sa ran Shirin yaƙi da cutar zai fitar ta rahotonsa game da yawaitar kamuwa da cutar a duniya.

Afrika ta kudu ita ce ƙasa da ta fi yawan mutane da ke ɗauke da Cutar HIV a duniya kuma kafin watan maris na wannan shekarar ita ce ƙasar da ta fi samun tallafin yaƙi da cutar daga Amurka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tallafin da Amurka ta bayar a baya ya taimaka wajen rage kamuwa da cutar da kashi sittin cikin dari tun shekara ta 2000.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC