Wata tankar man fetur da a ke yi mata gyaran walda ta kama da wuta tare da kashe mai aikin mai suna Kabiru Ibrahim, a Garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, a wani gareji da ke maƙwabtaka da babban ofishin ’yan sanda da ke Garin, da ke yankin ƙaramar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
Wani da ya shaida lamarin mai suna Ahmad Bunkau ya shaidawa Aminiya cewa, yana cikin masallaci Juma’a da ke kusa da wajen sai ya ji ƙara, sannan bayan ya fito waje sai ya ga tankar na ci da wuta.
Ya ce, tankar ta yi ta yin ƙara akai-akai na kamar tsawon minti 30 kafin jama’a suka samu nasarar kashe wutar. Wata majiyar ’yan sanda daga garin ta shaidawa Wakilinmu cewa, an nemi ɗauki daga jami’an Hukumar kashe gobara da ke Garin Sabon-Wuse da ke ƙaramar Hukumar Tafa ta jihar Neja amma ba tare da nasara ba, kasancewar yankin da abin ya faru na jihar Kaduna.
Wani jami’in ɗan sanda a ofishinsu na Tafa ya ce, ƙarar fashewar motar tankar ta tayar da hankali a ofishinsu, inda a cewarsa da farko su ka zaci hari ne na bam, lamrin da ya sa su ka yi ta gudu.
Sai dai ya ce daga bisani babban jami’in ’yan sanda na ofishin wato DPO, mai suna SP Ibrahim Idris ya jagorance su zuwa wajen don bada agaji, sannan bayan kashe wutar suka ɗauki gawar mai waldan tare da ajiyeta a asibitin tunawa da Umaru Musa Yaradua da ke Garin Sabon-Wuse.