Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta yi karin haske a game da taron da za ta gudanar tsakanin bangaren zababben shugaban kasa da kuma zababbun ‘yan majalisun tarayyar a Abuja.
Rahotanni dai sun bayyana cewa taron na da alaƙa da yunƙurin raba muƙamai a majalisar ƙasa ta 10 da za a kafa, a ƙoƙarin hana sake aukuwar abin da ya faru a 2015.
To sai kuma mai magana da yawun jam’iyyar na kasa Malam Bala Ibrahim, ya shaida wa manema labarai cewa, an kira wannan taron ne da zummar a yi tattaunar ‘yan cikin gida.
Ya ce taron zai kasance ne tsakanin shugaban ƙasa mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisun tarayyar na jam’iyyar ta APC inda za a tattauna yadda za a yi aiki tare da kuma samun damar aiwatar da manufofin jam’iyya ba tare da an fuskanci wata matsala ba.
Malam Bala Ibrahim, ya ce, Ba za a bayyana jadawalin abubuwan da za a tattauna a taro kai tsaye ba har sai an zo wajen taron, to sai dai kuma akwai mutanen da ke tsokaci kan abubuwan da suke gani za a tattauna a taron.
Ya kara da cewa maganar da ake yadawa cewa za a tattauna a kan yadda za a raba mukaman majalisun tarayya, ai babu wani abu da ya nuna cewa hakan za a tattauna a wajen taron, to amma idan har wannan batu ma ya taso a wajen taron ai ba wani abu bane na mamaki ko kuma ace an yi riga malam masallaci bane.
Mai Magana da yawun jam‘iyyar ta APC, ya ce duk wani rade-radi da ake a kan abin da ake gani wannan taro zai kunsa, ba haka bane, wannan taro sirri ne na jam’iyya, domin ita jam’iyya a kullum tana duba irin matsalolin da ta fuskanta a baya ne don ta gyara.