Tinubu Ya Aiyana Dokar Ta Baci Kan Tsaro A Nijeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, yana mai bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an ‘yansanda da na soja.

Shugaban wanda ya bayar da umarnin yayin wani jawabi a fadarsa, ya bai wa rundunar ‘yansandan ƙasar umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai 20,000.

Ya ce adadin sababbin jami’an da za a ɗauka yanzu ya zama 50,000, bayan umarnin da ya bayar ranar Lahadi na ɗaukar 30,000.

Ɗaya daga cikin mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya faɗa wa BBC cewa dokar na nufin ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro a faɗin Najeriya.

Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka ta Forest Guard.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ‘yanta’adda da ‘yanfashi daga dazuka”.

“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.