Tinubu ya ce za a saka kyamarorin tsaro fiye da 5,000 a Filato

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta saka kyamarorin tsaro masu amfani da fasahar AI fiye da 5,000 domin taimaka wa jami’an tsaro yaƙi da matsalar tsaro a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar.

Shugaba Tinubu ya bayyana matakin yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Alhamis.

Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da wasu mahara suka kai hari ƙauyen Angwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa tare da kashe mutane.

Shugaba Tinubu ya ce minsitan sadarwar zamani da tattalin arziki, Bosun Tijjani ne zai kula da saka kyamarorin tare da hadin gwiwar gwamnatin Filato da jami’an tsaro.

”Za a fara saka kyamarorin ne daga birnin Jos sannan a faɗaɗa aikin zuwa sauran sassan jihar, kamar yadda aka saka jihohin Legas da Enugu”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Shugaban na Najeriya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da alƙawarta farauto maharan.

“Na yi muku alƙawarin cewa irin wannan al’amari ba zai sake faruwa ba,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci ministan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da babban hafsa sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu da kuma babban sifeton ƴansandan ƙasar, Olatunji Disu, su “tabbatar da kamo waɗanda suka aikata kashe-kashen” na waɗanda ba su ji ba su gani ba.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC