Tinubu ya gana da shugaban Chadi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙucnin shugaban Chadi Idriss Déby a ranar Alhamis.

Sun yi ganawar ce cikin sirri a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, inda ake sa ran sun tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da kuma haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Ganawar na zuwa ne kafin tafiyar shugaba Tinubu jihar Filato inda yaje ya jajanta game da kashe-kashen da suka faru.

Najeriya da Chadi na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi.

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .