Tinubu ya isa Abu Dhabi don halartar taron makamashi

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar wani taron makon makamashi.

Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya samu tarba daga ministan harkokin wajen ƙasar UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, da jakadan UAE a Najeriya a ƙasar, Salem Saeed Al-Shamsi.

Shugaban Tinubu ya isa Abu Dhabi ne daga Turai, inda ya yi wani ɓangare na hutunsa ƙarshen shekara, inda ya tattauna da shugaban ƙasashen Rwanda da na Faransa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Fadar shugaban Najeriyar ta ce sarkin UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci Tinubu taron, wanda shugabannin duniya da ƙwararru da ƙungiyoyin fararen hula ke tattauna batutuwan da suka shafi makamashi da yadda za a inganta shi.

Post masu alaƙa

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi zuwa shekarar 2060.

Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu

Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe